An Tsaurara Tsaro a Manyan Kasuwanni Kano a yayin Zanga-zanga

FB IMG 1722516989091

A yayin gudanar da zanga-zangar lumana a garin Kano,an girke Jami’an tsaro a wasu Manyan Kasuwanni dake kantin kwarai da ta Sabon gari.

An baza Jami’an tsaron ne dan hana Matasa bata gari,abkawa Kasuwannin don gujewa samin Asarar dukiyoyin Al’umma.

Jami’an tsaron sun saka shigaye a duk wata hanyar dazata  ba matasan samun  kutsawa cikin Kasuwannin.

Masu zanga-zangar wanda mafi akasarin su matasa ne,na dauke da kwalaye dake dauke da irin koke-koken su a rubuce, suna zagayawa cikin birnin na Kano.

Tunda farko dai Matasan sunje gidan gwamnatin Kano,inda suka bukaci Gwamna Abba  Kabiru Yusuf  ya fito yayi masu bayani.

A yayin hada wannan rahoton wasu matasan na bakin kofar gidan gwamnatin na Kano,inda wasu suka wuce dan gujewa abin da ka iya faruwa na tsautsayi.

Wasu matasan masu zanga-zangar da suka  sami damar yin ta’adi a shagunan al’umma,sun tafi Dan-agundi,inda suka gamu da wasu da sukayi kokarin kwace  kayan,a  inda aka sami damar kama wasu.

Jami’in hurda da Jama’a na rundunar ‘yansandan Kano AbduIlahi Kiyawa yace sunyi Nasarar kama wasu da suka fasa Shagunan dake titin Zariya,kuma zasu gurfanar dasu ga hukuma.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *