Gwamnan Abba Kabir ya nada sabon shugaban ma’aikatan jihar Kano

FB IMG 1696417537151 edit 786631287899

Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya amince da nada Alhaji Abdullahi Musa a matsayin sabon shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar.

Alfijir Labarai ta rawaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikewa manema labarai.

Yace nadin nasu na zuwa ne bayan da tsohon shugaban ma’aikatan jihar kano Usman Bala ya kammala aikin sa , Inda yayi ritaya daga aikin gwamnati tun a watan mayun shekara ta 2023, kamar yadda doka ta tanada .

Sanarwar ta ce Alhaji Abdullahi Musa kwararen ma’aikacin gwamnati ne da yayi aiki a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin jihar kano, kuma haifaffen karamar hukumar Kiru ne.

Sabon Shugaban Ma’aikatan gwamnatin jihar kano Abdullahi Musa ya taba zama babban Sakatare a gidan gwamnatin jihar kano da majalisar zartarwa ta jihar da kuma ma’aikatar ayyuka na musamman da dai sauransu.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bukaci sabon shugaban ma’aikatan da ya gudanar da aikin sa cikin kwarewa da bin dokoki da ka’idojin aikin gwamnati.

IMG 20231127 WA0001
New Head of service

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *