Ya roƙi alƙalai da kada su damu da ra’ayin masu Zanga-Zanga, yayin da suke yanke hukuncin a kan batutuwa
Alfijir Labarai ta rawaito babban alkalin alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola, ya mayar da martani kan zarge-zargen nuna son kai a kan batutuwan da suka shafi zaben 2023.
kotunan zabe da kotun daukaka kara sun soke zabukan da aka yi na masu rike da mukaman gwamnati da aka zaba a babban zaben da ya gabata.
Kotu ta kori wasu gwamnoni da Sanatoci da ‘yan Majalisar Wakilai saboda korafin da jam’iyyun adawa suka yi.
Sai dai magoya bayan shugabannin da aka kora dai sun zargi bangaren shari’a da goyon bayan jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar.
A nasa bangaren da yake magana a wajen bude zama na musamman na shekarar shari’a ta 2023/2024, da kuma rantsar da sabbin manyan lauyoyin Najeriya 58, Ariwoola ya bukaci alkalai da su tsaya tsayin daka, yana mai cewa bai kamata a ruguza tunanin shari’a ba.
Ya roƙi alƙalai da kada su damu da ra’ayin masu Zanga-Zanga, yayin da suke yanke hukuncin a kan batutuwa.
Ya kara da cewar, yanzu ya zama dole a yi la’akari da cewa ra’ayin jama’a, ba zai sa ku kauce daga kasancewa a matsayin doka ba wajen yanke hukunci kan shari’o’in da ke gaban ku.
Daily Post
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp