Wata kotun shari’ar Musulunci ta bayar da umarnin yanke kafar hagu da hannun daman wanda ake tuhuma bisa laifin sata.
Alfijir Labarai ta rawaito babban Kadi na Kano, Tijjani Yusuf -Yakasai, ya kafa wani kwamiti da zai duba shari’ar wani dattijo da ke jiran yanke masa hannu na tsawon shekaru 18 a gidan yari.
Khadi Yakasai ya kuma bayar da belin wasu mutane 147 da ke da kananan laifuka a gidajen yari biyu a Kano.
A ranar Litinin, an bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar gidan yari ta Kano, SC Musbahu Kofar-Nasarawa ya fitar.
Ya ce an yanke shawarar rage cunkoso tare da ‘yanto wadanda ke cikin gidajen yarin Kano.
A cewarsa, kwamitin ya kunshi alkalai shida a karkashin wani alkalin kotun shari’ar musulunci, Ibrahim Sarki-Yola.
“Kotun Shari’ar Musulunci ta Kano ta bayar da umarnin yanke kafar hagu da hannun dama na mai laifi a hukuncin da ta yanke kan aikata laifin sata,” in ji Ibrahim-Yakasai.
“Kwamitin zai duba shari’ar zaman gidan yari na tsawon shekaru 18 a Kano ba tare da zartar da hukuncin ba.”
Yakasai ya bukaci fursunonin da aka saki da su kasance masu kyau da kuma nisantar duk wata rashin da’a da za ta kai ga a sake kai su gidan yari.
A nasa bangaren, kwamandan gidan yari na Kano, Suleiman Mohammed-Inuwa, ya godewa babban Kadi da ya rage cunkoso a gidajen.
(NAN)
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp