Gwamnatin Kano Ta Sanya Hoton Muhd Sanusi II A Coronation Ta Bayyana Dalili

Dakin taro na Coronation mai dimbin tarihi da ke Kano yana da mahimmaci na musamman a cikin abubuwan tarihi na birnin domin tun da farko an gina shi ne domin nadin sarautar Sarkin Kano na 14, Malam Muhammadu Sanusi.

Alfijir Labarai ta rawaito Sanusi Bature Dawakin Tofa babban sakataren yaɗa Labarai na Gwamnan kano ya ce zauren wanda a cikin sa aka mik shaidar kama aiki ga Muhammad Sanusi II, bayan rasuwar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero a shekarar 2014 a lokacin gwamnatin Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso, yanzu haka ana ci gaba da gyare-gyare domin dawo da martabar dakin taron dake fadar gwamnatin jihar kano.

Wani muhimmin abu na wannan aikin na gyare-gyare shi ne mayar da hoton Sarki na 14, Malam Muhammadu Sanusi, a cikin zauren, hoton zai kasance a dakin har abada, don tunawa da sarautar tsohon sarki.

Gyaran da ake ci gaba da yi na nufin baiwa zauren Coronation gyaran fuska da ake bukata, tare da kiyaye muhimmancin tarihi da al’adunsa.

Bature ya tabbatar da cewa gyaran zauren ya hada da dawo da hoton mai girma sarki na 14.

Zauren taro na Coronation yana da kima sosai ga al’ummar Kano, kuma gyaran da aka yi masa na nuna aniyar gwamnatin na kiyaye dimbin tarihi da al’adun gargajiya na mutanen Kano.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

2 Replies to “Gwamnatin Kano Ta Sanya Hoton Muhd Sanusi II A Coronation Ta Bayyana Dalili

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *