Tankin Ruwa Ya Ragargaje Wani Matashi Da Ke Bacci

Alfijir Labarai ta rawaito wani Tankin ruwa a sama ya rikito kan wani matashi wanda sanadiyar haka ya rasa ransa.

lamarin ya faru ne a unguwar Ikotun-Ekpe da ke birnin na Ikko.

Jamal Nureini mai shekaru 20 shine wanda Ibtila’in ya rutsa da shi, yana kwance ne a cikin daki a gidan su, sai kawai tankin sama na ruwa na makotakansu ya fado daga sama akan dakinsa lokacin yana bacci, ya kuma burma kwanon dakin ya fado ya murkushe shi.

Kakar matashin Alhaja Yemisi Odejinmi wanda ta ke rayuwa da jikan nata a gidan, ta ce, wannan al’amari ya yi matukar sanya rayuwarta cikin garari.

“Ina kokarin idan Jamal ya tashi daga bacci za mu tafi fadar basaraken Legas don neman shaidar dan jiha saboda an bukaci Jamal da ya kawo a makaranta saboda ya samu gurbin karatu a jami’ar jihar Legas, amma yanzu ga abin da ya faru” inji kakar marigayin.

Gaskiya Tafi kwabo

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *