Alfijir Labarai ta rawaito Wata kotun majistare da ke jihar Kano ta yanke wa wata mata mai suna Elizabeth Gift hukuncin daurin watanni 18 a gidan yari bayan da ya aika mata ta ajiye kudin. a banki.
Mai gabatar da kara, Barista Jamilu Abubakar, ya shaida wa kotun cewa, a watan Afrilu ne mijin nata mai suna Benefice ya aika wadda ake kara a banki domin ta ajiye wadannan kudade a banki, amma sai ta dawo ta ce wasu sun yi amfani da makamai ne suka karbo mata kudin.
Ya ce binciken da aka yi ya nuna cewa ba a sace mata kudin ba, kuma da gangan ta kai wa wasu mutane da yarjejeniyar cewa za su kara mata kudi.
Wanda ake tuhumar ta amsa laifinta.
Alkalin kotun, Halima Nasir, ta yanke mata hukuncin daurin watanni 18 a gidan yari tare da umarce ta da ta biya mijinta N2,050,000.
Sai dai alkalin kotun ya ba ta zabin tarar N50,000 ko tsawon watanni 18 a gidan yari.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
𝐓𝐨𝐟𝐚 𝐚𝐥𝐥𝐚𝐡 𝐲𝐚𝐬𝐡𝐢𝐫𝐲𝐚,𝐤𝐢𝐫𝐚𝐬𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐝𝐚 𝐳𝐚𝐤𝐢𝐜𝐢 𝐚𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐬𝐚𝐢 𝐦𝐢𝐣𝐢𝐧𝐤𝐢.
Gaskiya muna jin dadin labarunku amma gaskiya a runka gyara lead na labarun
Masha Allah
Muna godiya za a kula
Allah kyauta