Alfijir Labarai ta rawaito Hukumar da ke Kula da Rabon Tattalin Arzikin Kasa (RMAFC), ta amince da yin karin albashi na fiye da kaso 114 cikin 100 ga zababbun ’yan siyasa da alkalai da masu rike da mukaman gwamnati.
Daga cikin wadanda za su amfana da sabon karin akwai Shugaban Kasa da Mataimakinsa, Gwamnoni da Mataimakansu da kuma ’yan majalisa da ma’aikatan bangaren shari’a.
RMAFC ce dai hukumar da aka dora wa alhakin kayyade zababbun masu rike da mukaman siyasa da Ministoci da Kwamishinoni da mashawartan Shugaban Kasa da Gwamnoni da sauran wadanda aka ambata a sassa na 84 da kuma 124 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
Tuni dai hukumar ta bukaci Majalisun Dokoki na Jihohi da su gaggauta yin kwaskwarima ga dokokinsu, ta yadda za a sami damar aiwatar da sabon karin.
A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), Shugaban hukumar ta RMAFC, Muhammadu Shehu ne ya yi kiran a Birnin Kebbi ranar Laraba, kuma ya sami wakilcin Kwamishinan hukumar, Rakiya Tanko-Ayuba.
Ya ce karin ya fara aiki ne tun daga ranar 1 ga watan Janairu, kuma an yi shi ne daidai da tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulki.
Ya ce rabon da a yi irin wannan karin albashin tun a shekara ta 2007. Ya ce karin ya zama wajibi saboda abin da ake biyansu ya dace da yanayin tattalin arzikin kasa na yanzu.
Aminiya
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
Allah sarki civil servants. Su kuma ko su mutu ko suyi rai babu me ko kallonsu. Allah ya dubesu Amin
Allah sarki su kuma sojojin najeriya ko oho gasucan adaji iyalansu na kewar su abariki ,bahutu ba baccin kirki Babu albashin da zai isa biyan kudin makrantar ‘ya’yan su kullun cikin maneji allahu akbar sojan Najeriya Allah ya tausaya musu amin