
Alfijr ta rawaito Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da hannu wajen tono gawarwaki daga kaburbura da kuma cire sassan jikinsu domin gudanar da ibada a jihar Ogun.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi a ranar Lahadi ya bayyana cewa, an kama wadanda ake zargin ne a ranar Asabar, 11 ga watan Maris, 2023.

A cewar kakakin wadanda ake zargin sune; Oshole Fayemi mai shekaru 60, Oseni Adesanya mai shekaru 39 da Ismaila Seidu mai shekaru 30 da Oseni Oluwasegun mai shekaru 69 da Lawal Olaiya mai shekaru 50.

An kama su ne biyo bayan wani rahoto da ya jagoranci jami’in ‘yan sanda na shiyyar Odogbolu, Godwin Idehai da mutanensa zuwa wurin su, maboya jim kadan kafin su fara girbin sassan jikin mutane a garin Ososa.
Oyeyemi ya ce wadanda ake zargin sun amsa cewa suna cikin harkar tono gawarwaki daga kaburbura.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai