Alfijr ta rawaito Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dakatar da zaben Sanatan Enugu ta gabas saboda mutuwar Oyibo Chukwu, dan takarar jam’iyyar Labour.
Shugaban hukumar ta INEC, Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a yayin da yake ganawa da manema labarai a cibiyar tattara sakamakon zabe ta kasa da ke Abuja.
An kashe Chukwu tare da kone shi a Amechi Awkunanaw da ke karamar hukumar Enugu ta kudu a ranar Laraba bayan da ‘yan bindiga suka bude wa ayarin motocinsa wuta.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇