Ƙungiyar Ma’aikatan Rediyo, Talabijin, Wasan Kwaikwayo da Fasaha (RATTAWU) reshen Jihar Kano ta yabawa Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa, bisa rawar da ya taka wajen gyaran motar ƙungiyar da ta lalace tsawon lokaci.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata shugaban RATTAWU na Jihar Kano, Kwamared Babangida Mamuda Biyamusu, ne ya ya fitar ga manema labarai a jihar Kano.
Ya ce motar ƙungiyar ta daɗe bata aiki sakamakon matsalar Inji, lamarin da ya janyo wa mambobinta cikas wajen gudanar da ayyukan ƙungiya da sauran hidimomin shugabancin kungiyar.
Kwamared Biyamusu ya bayyana matakin da Sunusi Bature ya ɗauka a matsayin abin a yaba, yana mai cewa gyaran motar ya dawo da ita bakin aiki tare da rage matsalolin sufuri da ƙungiyar ke fuskanta.
A cewarsa, “A madadin dukkan yayan kungiyar RATTAWU na Jihar Kano, muna miƙa godiya ta musamman bisa wannan karamci. Gyaran motar zai taimaka matuƙa wajen ƙara inganta ayyukanmu da sauƙaƙa gudanar da shirye-shiryen ƙungiyar.”
Ya tabbatar da cewa mambobin RATTAWU za su ci gaba da taka rawar gani wajen wayar da kan al’umma da yaɗa bayanai kan manufofi, shirye-shirye da ayyukan ci gaban da gwamnatin jihar ke aiwatarwa.
Shugaban ƙungiyar ya kuma yabawa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa jajircewar gwamnatinsa wajen bunƙasa jihar karkashin manufar “Kano First”, wadda ya ce ta kawo sauye-sauye masu ma’ana ga rayuwar al’umma.
Ya bayyana Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin shugaba Wanda ya ke da kusanci da jama’a kuma mai bai wa kafafen yaɗa labarai muhimmanci, wanda gwamnatinsa ke aiwatar da tsare-tsare da shirye-shiryen da suka mayar da hankali wajen inganta walwalar al’umma da hanzarta ci gaban jihar.
A ƙarshe, Kwamared Biyamusu ya sake jaddada kudirin RATTAWU na ci gaba da inganta ƙwarewa da bin ƙa’idojin aikin jarida tare da mara wa duk wasu shirye-shiryen ci gaban Jihar Kano baya.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t