Zargin Karkatar Da Shinkafa: EFCC Zata Fara Bincike Kan Shugaban ma’aikatan Fadar Gwamnatin Kano Sagagi

Screenshot 20240814 102536 InShot

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta tabbatar da karbar korafin da wata Kungiya ta kai mata kan zargin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kano, Shehu Wada Sagagi da karkatar da shinkafar da gwamnatin tarayya ta kawo jihar.

Alfijir labarai ta ruwaito koken, wanda kungiyar Arewa APC Merger Group ce ta shigar da shi, wanda shugabanta na kasa Hon. Musa Mujahid Zaitawa ya sawa hannu, ya yi zargin cewa Sagagi na da hannu wajen karkatar da tallafin shinkafa na Gwamnatin Tarayya ta kawo domin raba wa ga al’ummar Jihar Kano.

A cewar wasikar da aka aike wa shugaban hukumar ta EFCC, kungiyar ta yi ikirarin cewa sahihan rahotanni daga kafafen yada labarai da majiya mai tushe sun nuna cewa Sagagi ya boye shinkafar ne a daya daga cikin gidansa da ke Gandun Albasa Quarters, Kano.

Wasikar ta ci gaba da cewa matasa sun kutsa cikin gidan tare da kwashe shinkafar ne yayin da ake gudanar da Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa.

Kungiyar ta yi Allah-wadai da wannan aika-aika ta Sagagi, inda ta bayyana hakan a matsayin rashin tausayi da ma da cin amanar jama’a.

Sun bukaci hukumar ta EFCC da ta yi bincike sosai kan lamarin tare da tabbatar da cewa an yi adalci, tare da jaddada amincewarsu da kudurin hukumar na tabbatar da doka da kare muradun ‘yan kasa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *