Katobara! Yadda Wasu Ƴan Uwa Suka Binne Ƙaramin Ƙanin Su Dan Shekara 16 Da Ransa A Zariya

FB IMG 1703222676383

Wani lamari mai ban al’ajabi da tayar da hankali, wani rahoto ya nuna yadda wasu ƴan uwa biyu suka binne ƙaramin Ƙanin su mai shekara 16 da ransa, mai suna Abubakar sakamakon ɓatan waya a garin Zariya dake jihar Kaduna.

Alfijir labarai ta ruwaito yan sanda sun yi nasarar kama waɗanda suka aikata laifin, ɗaya mai shekaru 22 da kuma 18, bayan da wani mutum ya hangi kan Abubakar yana reto a rami cikin wani kango.

A cewar shaidun gani da ido, ‘yan’uwan sun samu rashin jituwa dalilin wata waya da ta bata a Abuja, inda suke aiki.

WIKKI TIMES ta ruwaito cewa ‘yan uwan sun biyo Abubakar har Zariya inda suka binne shi da rai a matsayin azabtarwa.

Kwamishinan ma’aikatar jin dadin jama’a da ci gaban jama’a na jihar Kaduna, Rabi Salisu ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar.

“Sai da suka ɗauke yaron, sannan suka kulle bakinsa, sannan suka binne shi a rami, kansa ne kawai a waje. Ban taba ganin an binne wani da rai a fili ba in ba a fim ba. In ji wani ganau.

Yaron mai suna Abubakar dan shekara 16 ‘yan uwansa sun yi masa wannan azaba ne saboda bacewar wayar.

“Sun tona rami, inda suka daure hannayensa bayan sun rufe bakinsa, sannan suka binne shi, kansa kawai suka bari a waje a lulluɓe da tsumma a cikin wani kango kusa da wata gona. Wani bawan Allah ne da ya ji yaron yana tari wanda hakan ya jawo hankali wasu manoma har suka ceto yaron.

“Wadanda suka aikata laifin da mai shekara 22 da dan uwansa, dan shekara 18 ne ƴan sanda sun yi nasarar kama su..

Gwamnati ba za ta dauki hakan da wasa ba, wajen kare hakkin yara da sauran wadanda ake tauye hakkinsu a jihar Kaduna,” inji Rabi Salisu

Shima da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Mansir Hassan, ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike, inda ya ce wadanda ake zargin suna tsare kuma za a gurfanar da su a gaban kotu nan ba da jimawa ba.

A wata sanarwa da ma’aikatar kula da ayyukan jin kai da ci gaban jama’a ta jihar, ta fitar a ranar Laraba, ta bayyana cewa ta dauki kwakkwaran mataki bayan afkuwar lamarin.

Sanarwar ta kara da cewa, “Wanda aka binne, Abubakar Aliyu, ya tsallake rijiya da baya, kuma tuni aka kubutar da shi. ‘Yan sanda sun kama wadanda ake zargin.

“Jami’in jin dadin jama’a da ke Zariya ya ziyarci yankin da lamarin ya afku domin duba halin da ake ciki tare da bayar da tallafin da ya dace. Ma’aikatar ta tabbatar wa jama’a cewa za a yi adalci kuma za su ci gaba da sanya ido sosai kan lamarin.

“Kuma Gwamnatin jihar Kaduna ta yi Allah-wadai da wannan aika-aika da kakkausar murya tare da jaddada kudirinta na kare hakki da walwalar ƴan kasa musamman kananan yara.”

Inda Ranka

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *