Zargi:Gwamnan Babban Bankin Najeriya Ya Kwashe Tiriliyan 80

Alfijr ta rawaito Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure wanda shine sakataren kwamitin na musamman da shugaba Buhari ya nada ya bayyana cewa wasu hukumomi da abin ya shafa suna kokarin hanashi yin aikinsa.

Gudaji ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da ya yi take yawo a shafin sada zumunta, inda yake cewa mutanen da abin ya shafa sun hanashi mikawa shugaba Buhari rahoton binciken da ya yi.

“Kwamitin mu ya fara gano wasu tiriliyan 3.9 na naira da kuma biliyan dari da saba’in da daya na dalar Amurka a 2020, akwai bashi da aka baiwa bankuna wanda yakai N23.4 tiriliyan da kuma bashi da aka baiwa gwamnati N23 tiriliyan.” In ji shi.

Ya Kara da cewar “Muna zargin bankin CBN da rantawa gwamnatin Najeriya kudinta na kanta domin babban bankin na CBN bashi da hanyar da zai samu wadannan kudaden haka in ba ta hanyar cajin kudin cira da ajiya a asusun banki ba”.

“Kusan shekara shida ana yaudarar gwamnati da wannan Badakalar, domin ba’a saka kudaden na cajin cira da kuma ajiyar kudi a asusun gwamnati”.

Ya ce “Hankalin gwamnan CBN da kuma ministan shari’a da alkalin alkalai ya tashi sakamakon binciken da na gudanar”.

Kazaure ya zargi ministan shari’a da rubuta takarda domin dakatar dasu akan wannan binciken da suke gudanarwa.

Haka kuma ya zargi protokol na shugaban kasa da hanashi ganin shugaban kasa domin mika masa sakamakon binciken, bayan shugaban ya umurcesu da su dinga zuwa suna kawo masa rahoton duk bayan sati daya.

Daga karshe ya bayyana sakamakon binciken shi cewa tabbas wadannan kudaden akwai su kuma kudaden gwamnati ne, babu shakka wadannan kudaden na iya biyan duk basusukan da ake bin Najeriya.

Ya Kara da cewa “Ko kadan ban karaya ba domin ina ji a jikina wannan dama ce da shugaban kasa zai bani domin kama gwamnan CBN in kulle tare da duk masu hannu cikin wannan badakalar,” inji Gudaji.

Sai dai a nasa bangaren Malam Garba Shehu, shi ne mai magana da yawun shugaban kasar Najeriya ya yi karin bayanin kan wannan batun ga BBC

Ya kara da cewa wannan magana ta Gudaji Kazaure ba za a ce kwamiti ne ba. E, ya kafa kwamiti da kansa kuma ya nada jami’ai a ciki har da alkalin alkaln Najeriya da wasu mambobi, tabbas ya sami shugaban kuma ya nuna masa kwato kudade na kasa za a yi.”

Garba ya ce duk mutumin da ya gaya wa Buhari cewa zai kwato kudi, zai ce masa Allah-san-barka, sai dai ya musanta cewa shugaban kasa ne ya kafa kwamitin:

“A zahirin gaskiya, duk wanda ya san yadda gwamnati ke tafiya, babu yadda za a ce shugaban kasa a bangaren gwamnati ya kafa kwamiti ya ba wa dan majalisa sakatare, ya kuma kira alkalin alkalai ya nada shi mamba! Ai an yi wa tsarin mulki karen tsaye.

Ya ce kwamiti haramtacce ne, “ba shi da hurumi a doka, shi yasa Shugaba Muhammadu Buhari yace a rusa shi, a kuma kafa sabo wanda ke karkashin ministan shari’a.”

Ya kuma bayyana mamakinsa kan yawan kudaden da Gudaji Kazaure ke ambatowa a kalamansa da ke cewa biliyoyin daloli ne aka yi badakkalarsu.

“Wannan zargi na tiriliyan 160 da yake cewa sun salwanta, ina kudin suke? Tiriliyan 160 fa.”

Ya ce idan aka tattara dukiyar da dukkan bankunan Najeriya wuri guda, ba su kai kashi daya cikin uku na kudaden ba.

[07/12, 11:35 pm] Musa Best Seller: Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Best seller Channel
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

One Reply to “Zargi:Gwamnan Babban Bankin Najeriya Ya Kwashe Tiriliyan 80”

  1. Mudai kullin muna rokon Allah yarona asirin 6arayin kasarmu dakuma Wanda sukedasa hannu acikin cutarda kasarmu muna rokon Allah duk Wanda baburinsa Nigeria tacigababa kada Allah yabashi damarda zai jagorancemu Allah kashiryi shugabanninmu kaganardasu kayiroko da hannayansu kasaitasu akan hanya madaidaiciya karabasuda sanzuciya kabasu ikon kawowa kasarmu cigaba da wanzuwar arziki sabida annabi muhammad s.a.w.ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *