Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Alfijr ta rawaito sakamakon irin fitowar da Mata sukayi kwansu da kwarkwatan su wurin jefa kuri’a a kasannan , ciki har da masu juna biyu .
A wata runfar zabe Mai lamba 001 a mazabar tsafe a karamar hukumar tsafe ,Allah yayi wa wata mai suna Shamsiya Ibrahim, rasuwa a lokacin da take kokarin jefa kuri’a.
Shamsiya Ibrahim,haifafar Tsafe ce, amma tana aure ne a garin kwatarkwashi, tazo tsafe ne don jefa kuri’a a runfar ta dake Asibitin kutare.
A zantawarmu da Adamu Yusif tsahon DPO ya bayyana ma wakilin mu cewa, Shamsiya Ibrahim tazo bata da lafiya shigowarta ke da yuwa runfar zaben sai ta kama aman jini ta baki ta hanci, hakan yasa a kaita Asibitin Dr Bawa da ke kusa da rumfar jefa kuri’ar.
Mutuwar Shamsiya Ibrahim ta girgiza masu jefa kuri’a a runfar zaben wanda yayi sanadiyar wasu suka fasa jefa kuri’ar saboda jimamin rashin.
A’isha Muhammad ‘yar uwace ga marigayiya Shamsiya Ibrahim ta bayyana ma wakilim mu cewa, lallai tayi kwana biyu bata da lafiya ashe a wajan zaben ne AlIah zai amshi Rayuwan ta Kuma tana dauke da juna biyu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux
Allah ya jikan ta