Bata-Gari Sun Cinna Wa Ofishin INEC Wuta A Kano Mutum 4 Sun Mutu


Alfijr ta rawaito Wasu bata-gari da ba a gano ko su wane ne ba sun cinna wa ofishin INEC na karamar hukumar Takai wuta.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi, bayan wani rikicin magoya bayan jam’iyyau ya balle.


Ya kuma ce an samu nasarar kashe wutar, kafin tayi ta’adi, amma “Duk da haka wasu sun samu rauni suna ma asibiti suna karbar magani, hudu kuma sun mutu.”

Rahotanni na nuna rikicin ya fara ne, yayin tattara sakamakon zaben karamar hukumar.

A nasa bangaren Kakakin rundunar ’yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce a dakin ajiye janareta aka cinna wutar, sai dai an samu kashe wa tun ba ta yi nisa ba.

Sai dai ya ce ba shi da masaniyar asarar rai ko daya.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

5 Replies to “Bata-Gari Sun Cinna Wa Ofishin INEC Wuta A Kano Mutum 4 Sun Mutu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *