Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ya ce sun samu rahoton wasu bata gari na shirin kona gidan gwamnatin jihar Kano.
Alfijir labarai ta rawaito CP din ya bayyana hakan ne yayin ganawar da yayi da shugabannin kafafen yada labarai da ta gudana a ranar Laraba, a shelkwatar rundunar dake Bamfai, yana mai cewa jami’ansu zasu dakile bata garin dake da dabi’ar neman kona gidan gwmnatin Kano.
Kwamishinan ‘yan sandan ya ce duba da yadda kotun koli zata fara sauraron karar zaben gwamnan jihar Kano a ranar Alhamis a Abuja, sun lura da yadda wasu bata gari suka fara bin shafukan sada zumunta suna yada labaran karya, a dan haka ya bukaci halatttun kafafen yada labaran da su kauracewa yin amfani da labaran karya da suke yawo a shafukan sada zumunta.
Kwamishina Gumel ya kuma yabawa kafafen yada labarai dake jihar Kano, duba da yadda suke baiwa rundunar hadin kai a ayyukanta na kiyaye rayuka da dukiyoyin al’ummar jahar dama kasa baki daya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp