Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Laraba 20/12/2023 – 06/06/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya rage wa matafiya rabin kuɗin shiga motar haya samfurin bas-bas, kuma kyauta fasinjoji za su shiga jirgin ƙasa.

Majalisar dattawa ta baiwa ‘yan sanda wa’adin awa 24 su gurfanar da shugaban hukumar rijistar kamfanoni CAC a gabanta.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ayyana kujerun Sanatoci biyu a matsayin waɗanda babu kowa.

Asibitin kwararru na jihar Kogi ya koka kan yadda likitoci ke wuyar samu a ‘yan kwanakin nan.

Jam’iyyar PDP ta sha alwashin hukunta tsohon gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da wasu ’ya’yanta kan yi mata zagon kasa a zaben 2023.

Sojoji sunyi gaggarumar nasara akan yan ta’adda a garin Kucheri dake karamar Hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Rundunar ƴan sandan jihar Taraba ta sanar da samun nasarar kashe ƴan bindiga uku tare da kuɓutar da wasu mutane da dama da aka yi garkuwa da su.

Sojoji sun ceto mutum 13 da ’yan bindiga suka sace, suka kama wasu mutane 11 dauke da makamai a Jihar Zamfara.

’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 11 a kauyen Kubuwo da ke Karamar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna.

Tsohon Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, ya yi murabus a matsayin ministan kwadago da samar da ayyukan yi.

Sheikh Meshal al-Ahmad al-Sabah, ya karbi rantsuwar fara aiki a matsayin sabon Sarkin kasar Kuwait.

Dalibai sun shigar da ƙara bayan an rage daƙiƙa 90 cikin lokacin jarabawa a Koriya ta Kudu.

Hukumomi a kasar Kongo sun yi alƙawarin ba za a katse sadarwar intanet ba yayin da ake zaɓe a ƙasar.

Kotu ta haramta wa Trump tsayawa takara.

Shugaban Hamas ya isa Alƙahira don tattaunawa kan tsagaita wuta a Gaza.

Shugaban Guinea Bissau ya nada sabon Firaminista bayan yunkurin juyin mulki.

Hukumar kwallon kafar Rasha ta kada kuri’ar kin amincewa da ficewa daga UEFA.

Dani Alves zai gurfana a gaban kotu bisa laifin fyade a watan Fabrairu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *