Yaya Makomar Ilimin Talakawan Najeriya? Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Ƙara Kuɗin NECO Zuwa Dubu 50.

IMG 225542 11726 1783806954207

A wani sabon mataki da ka iya jawo muhawara a fannin ilimi, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta amince da ƙarin kuɗin rajistar jarabawar NECO zuwa Naira 50,000 ga kowanne ɗalibi, matakin da zai fara aiki daga jarabawar SSCE ta shekarar 2027.

Ƙarin kuɗin rajistar jarabawar NECO zuwa kusan naira dubu 50 babu shakka ya sake tayar da tambayoyi masu nauyi kan makomar ilimin ‘ya’yan talakawan Najeriya.

A ƙasar da iyaye da dama ke fama da tsadar rayuwa, hauhawar farashi da ƙarancin kuɗaɗen shiga, irin wannan ƙari na iya ƙara nauyi a kansu. Wasu iyalai na iya shiga cikin tsaka mai wuya tsakanin biyan kuɗin rajistar jarabawa ko biyan wasu buƙatun yau da kullum kamar abinci da magani.

Idan iyaye ba za su iya biyan kuɗin rajistar ba, akwai yiwuwar daruruwan ɗalibai su rasa damar rubuta jarabawar a kan lokaci ko kuma su dakatar da karatu gaba ɗaya. Hakan na iya ƙara yawan yaran da ke ficewa daga makaranta, musamman a yankunan karkara da kuma cikin iyalan masu ƙaramin ƙarfi.

Duk da haka, tasirin hakan zai dogara da ko za a samar da tallafi, rangwamen kuɗi, ko wasu shirye-shiryen da za su rage nauyin da ke kan iyalai.
Saboda haka, akwai buƙatar gwamnati da hukumomin da abin ya shafa su yi la’akari da hanyoyin da za su tabbatar cewa ƙarin kuɗin ba ya hana ɗalibai samun damar ilimi. Ilimi shi ne ginshiƙin ci gaban kowacce al’umma, kuma duk wani mataki da zai iya rage damar matasa masu ƙwazo na samun ilimi ya cancanci a yi nazari a kansa tare da neman mafita da za ta kare muradun ɗalibai da iyayensu.

Tuni ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta fitar da wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 18 ga Yuni, 2026, inda ta sanar da amincewar Ministan Ilimi na ƙasa da ƙarin kuɗin rajistar jarabawar kammala sakandare ta NECO zuwa Naira 50,000 ga kowanne ɗalibi, daga shekarar 2027.

Takardar, wadda Daraktan Sashen Ilimin Sakandare na Ma’aikatar, Mista Adeniji Ibrahim, ya sanya wa hannu a madadin Ministan Ilimi, ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne bayan buƙatar da Hukumar Shirya Jarabawar WAEC ta gabatar na sake duba kuɗin rajistar jarabawar sakandare saboda hauhawar kuɗaɗen gudanar da jarabawa.

Haka kuma, takardar ta tuna cewa a wani taron da Ministan Ilimi ya yi da hukumomin shirya jarabawa a ranar 31 ga Maris, 2026, an tattauna batun ƙarin kuɗin rajista, inda Ministan ya bayar da umarnin cewa WAEC da NECO su kasance da daidaitaccen kuɗin rajista ga jarabawar SSCE.

Bisa wannan shawara, Ma’aikatar ta amince da sanya Naira 50,000 a matsayin sabon kuɗin rajistar NECO ga ɗaliban makarantu, wanda zai fara aiki daga jarabawar NECO SSCE (Internal) ta shekarar 2027.

Har ila yau, Ma’aikatar ta umarci Hukumar NECO da ta sanar da dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da gwamnatocin jihohi, makarantu, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki, domin su yi shirin aiwatar da sabon tsarin kuɗin rajistar.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fuskantar ƙalubalen hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa a Najeriya, lamarin da ka iya ƙara ɗora nauyi a kan iyaye da masu ɗawainiyar biyan kuɗin karatun ɗalibai. Sai dai gwamnatin tarayya na ganin cewa sake duba kuɗin rajistar zai taimaka wajen tabbatar da inganci da dorewar gudanar da jarabawar kammala sakandare a ƙasar.

Yakuke ganin makomar Ilimin Talakawan Najeriya Idan wannan kari ya fara aiki?

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *