Yan Daba Sun Bude Wuta Akan Masu Zabe Da Kuma Yadda Ake Hada Hadar Saiyan Kuri’u

IMG 20231111 131548

Wasu ’yan bangar siyasa sun bude wa jama’a wuta tare da sace kayan zabe a yayin da ake gudanar da zaben gwamnan jihar Bayelsa

Alfijir labarai ta rawaito Wasu ’yan bangar siyasa sun bude wa jama’a wuta tare da sace kayan zabe a yayin da ake gudanar da zaben gwamnan jihar Bayelsa.

’Yan bangar siyasanan sun kai harin ne a wasu rumfunan zabe a kananan hukumomin Ija ta Kudu da kuma Sabgama, insa suka rika harbe-harbe suna tafiya da kayan zabe.

Maharan sun fatattaki masu zabe suka kwashe kayan zaben a yankin Agorogbene, rumufanan zabe masu lamba 6, 7 da 8 gunduma ta 11 da kek Karamar Hukumar Ijaw ta Kudu.

Masu zabe sun nemin yin fito-na-fito da ’yan bangar siyasan, amma suka mayar da martani da harbe-harbe.

Da misalin karfe 9 na safe wasu bata-garin sun kai hari a cibiyar tattara sakamakon zabe inda suka yi awon gaba da kayan zaben biyar daga cikin mazau bakwai.

Hakazalika wakilinmu ya ruwaito yadda jama’ar jihar ke tattauna yadda ake musu alkawairn N5,000 idan suka zabi dan takarar da aka yi musu tayi.

Daya daga cikin rumfunan zabe a Ekiti. An yi Allah-wadai da yadda ake sayen kuri’u

A yayin da ake gudanar da zaben gwamna a Jihar Kogi an samu rahotannin sayen kuri’u a wasu rumufuna.

Wakilinmu ya ruwaito yadda jama’ar jihar ke tattauna yadda ake musu alkawairn N5,000 idan suka zabi dan takarar da aka yi musu tayi.

Wakilinmu ya samu mutane na tattauna wannan batu a rumfar zabe da ke Miami daura da Adankolo a garin Lokoja  inda ya ga wakilin wata jam’iyya na sanya ido domin tabbatar da jam’iyyar da masu zabe suka dangwala wa kafin biyan su.

Irin haka na faruwa a Angwa Pawa da ke garin na Lokoja, inda ake kiran musamman mata gefe a ba su kudi, wasu tun kafin ma su yi zabe.

IMG 20231111 131533
Hoto Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *