Yan Bindiga Sun Harbe Mahaifin Shugaban Karamar Hukumar Rimin Gado

Alfijr ta rawaito wausu yan bindiga da ba a tantanceba, sun kashe hakimi Maigari a karamar hukumar Rimin Gadoa jihar kano, Aih Dhiru Abba .

Sabon babban sakataren sharia na jihar Kano Abbas Sanusi, wanda kuma dane ga marigayin ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Marigayin Hakimi ne, sannan kuma mahaifin shugaban karamar hukumar Rimin Gado wato Barr Manniru Dahiru Maigari.

Marigayin ya rasu ne bayan da wasu yan bindiga da ba a tantanceba, suka kai masa hari har gidansa da sanyin safiyar lahadi, in da suka yi masa raunika daban daban! daga bisani suka hallakashi har lahira.

An yi jana idarsa da safiyar lahadi a kauyen Maigari da ke karamar hukumar Rimin Gado ta Kano, muna addu ar Allah bya jikansa da gafara ya bawa iyalansa hakuri.

Su kuma Allah bayyanasu, kuma ya shiryesu idan masu siriya ne.

hdrpl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *