Inalillahi waina ilaihir rajiun !!! Kwamittin Amintatu, Kwamittin Dattijai da Kwamitin riko na YAKASAI ZUMUNTA na mika jaje da alhini ga wadanda suka sami raunika lokacin da yan fashi da makami suka shigo yakasai a wannan satin.
Wannan sanarwa ta fito daga bakin shugaban riko na yakasai zumunta lokacin da yake jajantawa alummar unguwar bayan fitowarsu daga taron gaggawa akan faruwar abun.
Sannan shugaban rikon yakara dacewa wannan Babbar musibace a unguwar da karamar hukumar Birni dama jahar kano baki daya. Wannan shine lokaci na farko da aka shigo da bindigogi unguwar banyan lokuta da dama da sukanyi amfani da wukake da adda da sauran makamai.
Shugaban Alh. Sadisu ya jawo hankalin al’ummarsa ta yakasai sukara hakuri jami’an tsaro sunanan suna aiki tukuro, haka kuma YAKASAI ZUMUNTA tana tattaunawa da masu ruwa da tsaki na unguwar don samu bakin zaren dakuma gudun afkuwar abun anangaba.
Akarshe, yayi kira ga al’umma su kara hakuri susa ido sosai wajan kaiwa da komuwar jama’a idan sunga wani abu wanda basu yarda dashiba suyi gaggawar sanar da jami’an tsaro don daukar mataki. Haka kuma yaroki acigaba da addu’oin da akasaba na yau da kullum dana wata-wata da akeyi a masallatai don samun kyakkyawan zaman lafiya da karuwar arziki a unguwarmu mai albarka da jaha baki daya. Allah ya bamu lafiya da zama lafiya, Ma’assalam Nagode.
SADIQ LABARAN TANKO
(Danburan Kutumbawa)
Jami’in hulda da Jama’a
YAKASAI ZUMUNTA
08/07/2025
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD