Yadda Ta Kasance A Zaman Shari’ar Da Aka Fara Yiwa Alhassan Ado Doguwa

Alfijr ta rawaito Babbar Kotun Tarayya karkashin mai shari’a Muhammad Nasir Yunus  ya bayar da belin Naira Miliyan 500 ga Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai. Alhassan Garba Ado Doguwa da kuma masu tsaya masa guda biyu.

Wanda ake tuhumar yana gaban shari’a ne kan zargin laifukan da suka shafi hada baki, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, kisan gilla da kuma cin zarafin jama’a.

Tun da farko dai ya ki amsa laifinsa a lokacin da aka gurfanar da shi a gaban kotun majistare ta Kano mai lamba 54.

Lauyan sa Nuraini Jimoh (SAN) a ranar Litinin ya roki babbar kotun tarayya da ke Kano da ta bayar da belin wanda ake kara, yana mai cewa wanda yake karewa ba shi da wani laifi, bisa ga hakan, tanadin sashe na 35 sub 6 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (1999 kamar yadda aka gyara)

Hukuncin shari’a kan bukatar, mai shari’a Nasir-Yunusa da ke jagorantar shari’ar ya ba Sharadi kan wanda ake kara ya bada zunzurutun kudi har naira miliyan 500 tare da amintattun mutane 2.

A cewar kotun, wadanda za su tsaya masa, za su zama sarki mai daraja ta daya da duk wani babban jami’i a ma’aikatan gwamnati.

Hakazalika kotun ta umarci Doguwa da ya ajiye fasfo dinsa na kasa da kasa zuwa rajistar kotun har sai an fara shari’a.

Kotun ta kuma hana wanda ake kara zuwa mazabar sa a lokacin zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha da za a gabatar a ranar 11 ga Maris, 2023.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *