Alfijr ta rawaito Kotun kolin Najeriya ta dage ci gaba da sauraren karar kan shirin musanya naira na babban bankin Najeriya (CBN) har zuwa ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu domin sauraren karar.
Kotun kolin da ta saurari karar a yau ranar Laraba, kotun ta cika makil da wasu manyan lauyoyi da sauran gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi, Nasir El-Rufai da Yahaya Bello.
A zaman da ya gabata, Kotun ta dakatar da aiwatar da wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu na CBN daga yin kwangilar tsohuwar takardar kudi ta N200, N500 da N1,000.
Jihohin Zamfara, Kogi da Kaduna ne suka shigar da karar gwamnatin tarayya da kuma babban bankin kasa CBN.
Sauran jihohin da suka hada da Neja, Kano, Ondo, Ekiti, su ma sun nemi a shigar da su karar da aka shigar da CBN da gwamnatin tarayya.
An fara zaman kotun inda mai shari’a John Okoro ya jagoranci kwamitin mutum bakwai.
Ya ce bai kamata kotun ta yi watsi da shari’ar da kuma manufarta ba domin yana shafar ’yan Najeriya da ke fadin kasar.
Jihar Legas, ta hannun babban lauyanta, Moyosore Onigbanjo, ita ma ta nemi a shigar da ita karar
Jihar Bayelsa, karkashin jagorancin Damian Dodo, ita ma ta nemi a shigar da ita kara a matsayin wanda ake kara. Hakazalika, jihar Edo ta nemi a shigar da ita a matsayin wanda ake kara.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
mudai talakawan Nigeria munga ta kanmu
Allah ka bamu shuga banni na gari