Sakamakon zaman tattaunawa da aka yi ranar Alhamis 22/05/2025 tsakanin Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano Alhaji Abba Al-Mustapha da wakilan Kungiyar MOPPAN ta Jihar Kano Ado Ahmad Gidan Dabino, MON da Ismail Khalil Ja’en da Mubarak Abba da Hayatudden Yakubu da Shugabannin kamfanonin Alrahus Film Production da Abnur Entertainment da Maishadda Global Resources da kuma Alhayat International, an tattauna kuma an kai ga cim ma matsaya.
Matsayar ita ce, mun yarda masu shirya finafinai su ci gaba da kawo ayyukansu ana dubawa saboda a magance matsalolin da ake ta samu wanda ke jawowa har jama’ar garisuna kawo korafe-korafe ga hukumar.
Kuma Hukumar Tace Finafinai da dab’i tana kokarin samar da wata hanya da za a dinga duba wa mutane fim dinsu ta hanyar online.
Muna fata ‘yan uwanmu masu wannan sana’a ta fim za su bayar da goyon baya wajen tsaftace wannan sana’a tamu.
Allah ya yi mana jagora ya sa mu dace, ya hada kawunanmu.Amin.
Ado Ahmad Gidan Dabino,MON
Shugaban Kungiyar MOPPAN ta Jihar Kano
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan π
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
β΅β΅https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group ππ
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD