Yadda Ta Kasance A Taron Ecowas Kan Afkawa Jamhuriyar Nijar Da Yaki

A wani taro da aka yi a Accra, babban birnin Ghana a yau Alhamis, hafsoshin tsaron kasar sun ce sun shirya tsaf domin dawo da mulkin farar hula a Nijar.

Alfijir Labarai ta rawaito dakarun kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS, sun ce a shirye suke su shiga cikin rundunar jiran ko ta kwana da za ta iya shiga Nijar.

Bayan da jami’an tsaron shugaban kasar suka karbe mulki daga hannun shugaba Mohamed Bazoum, kungiyar ECOWAS ta bada wa’adin kwanaki 7 ga sojojin kasar da su maido da shugaban kasar ko kuma su fuskanci takunkumi, ciki har da yiwuwar daukar matakin soji.

Sai dai gwamnatin mulkin sojan ta kafe kan matakan na ECOWAS ta kuma sha alwashin tarar duk wani hari na kasashen waje

Bayan haka, kungiyar ta yankin ta bukaci hafsoshin tsaro na kungiyar mai mambobi 15 da su fara aiki da rundunonin tsaro.

A wani taro da aka yi a Accra, babban birnin Ghana a yau Alhamis, hafsoshin tsaron kasar sun ce sun shirya tsaf domin dawo da mulkin farar hula a Nijar.

A cewar gidan talabijin na Aljazeera, dukkan kasashe mambobin kungiyar in ban da wadanda ke karkashin mulkin soja da kuma Cape Verde sun yi alkawarin shiga cikin shirin na jirage.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *