Dan Kwallon Nijeriya Ahmed Musa Ya Sai Wa Karkuzu Gida Ya Bashi Kyautar Kudi

Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, ya cika alkawarin da ya yi na saya wa fitaccen jarumin wasan Hausa, Abdullahi Shu’aibu, wanda aka fi sani da Karkuzu.

Alfijir Labarai ta rawaito ɗan wasan ya kuma baiwa fitaccen jarumin tallafin Naira dubu 500 domin a yi masa magani.

Wannan tagomashi daga Musa na zuwa ne kwanaki kadan bayan da jarumin ya makance, inda ya shiga kafafen sadarwa ya na neman taimakon kudi.

Nan take kyaftin din na Super Eagles ya aika daya daga cikin abokansa, Abdullahi Ismail, wanda aka fi sani da Rockboy zuwa gidan Karkuzu.

Da ya ke magana kan wannan karimcin, Rockboy ya ce, “A ranar farko da Ahmad Musa ya ga bidiyon Baba Karkuzu da ya rika yaduwa a kafafen sada zumunta na yanar gizo, inda yake neman a taimaka masa ya je asibiti, Musa ya kira ni, duk da cewa ya yi nisa, yana Turkiyya, amma ya aiko da tsabar kudi naira dubu dari biyar, na kai wa Baba Karkuzu.”

A cewarsa, Musa bai tsaya a nan ba, sai ya bayar da umarnin a saya wa jarumin gida na tsakanin naira miliyan hudu zuwa biyar.

Alhamdulillahi yau (Talata) Ahmad Musa ya cika alkawari. Ya aika da kudi naira miliyan biyar da dubu dari biyar (N5.5m).

“an sai wa Karkuzu gida ya kai Naira miliyan 8, amma alkawarin da Musa ya yi na Naira miliyan 5 ne, kuma Baba Kazkuzu, ya kuma samu wasu kudade daga wasu mutane, wadanda aka yi amfani da su wajen cika wa a biya kudin gidan,” inji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *