Yadda Ta Kasance A Shari’ar Mutumin Da Ya Cinnawa Masallaci Da Masallata Wuta A Kano

FB IMG 1717155182395

Babbar kotun shari’ar Musulunci da ke zama a Kano ta ɗage sauraron ƙarar da take yi kan wani matashi da ya cinna wa masallaci wuta a jihar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da jikkatar wasu.

Idan zaku iya tunawa a ranar 15 ga watan Mayu ne mutumin da ake zargi a watsa fetur tare da cinna wa masallaci wuta sa’ilin da ake sallar Asuba a ƙaramar hukumar Gezawa ta jiharn Kano.

Ya zuwa yanzu lamarin ya haifar da asarar ran mutum 19, yayin da wasu ke ci gaba da samun kulawa a asibiti.

A lokacin zaman kotun na yau, alƙali ya bayyana cewa an samu lauyan da zai kare wanda ake zargi, inda ya buƙaci a tattara duk wasu bayanai da hujjoji da suka kamata domin miƙa wa lauyan.

Kotun ta ɗage shari’ar ne zuwa ranar huɗu ga watan Yulin 2024.

A zaman da kotun ta yi na farko, mutumin ɗan shekara 38 ya amsa laifin da ake tuhumar sa da shi a lokacin da kotu ta karanto masa su.

Kimanin mutum 40 ne aka yi ƙiyasin suna cikin masallacin a lokacin da lamarin ya faru.

Rudunar ƴansandan Najeriya a jihar Kano ta ce binciken da ta yi na farko-farko sun tabbatar mata cewa wanda ake zargin ya kai hari a masallacin ne sanadiyyar rikici game da rabon gado.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *