Kotun daukaka ƙara dake babban Birnin tarayya Abuja, mai kwamitin alkalai uku karkashin mai shari’a Uchechukwu Onyemenam, ta zauna a wannan domin sauraron bangarorin Abdullahi Sule na jam’iyyar APC da David Ombugadu na jam’iyyar PDP kan zaɓen gwamnan jihar Nasarawa, wanda kotun sauraron ƙarar zaɓe ta kwace kujerar gwamnan jihar daga hannun APC ta bawa PDP.
Alfijir Labarai ta rawaito Yayin zaman, Lauyan Gwamna Sule, Wole Olanipekun, ya roƙi Kotun ɗaukaka ƙara ta rushe hukuncin Kotun zaɓe, domin kuwa anyi musu rashin adalci na ƙin karban bayanan shaidun da suka gabatar tare da watsi da alƙaluman BVAS da aka miƙawa karamar kotun.
Sai dai shima Lauyan PDP da ɗan takararta, Kanu Agabi, ya roƙi Kotun ta kori ƙarar da aka ɗaukaka wacce ta kalubalanci hukuncin Kotun zaɓe, inda ya kafa hujja da hukuncin da kotun zaɓe ta yanke, ya ce a yayin da take yanke hukunci, karamar kotun ta yi cikakken bayani kan yadda ta cimma wannan
Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇
https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI
Bayan kammala sauraron kowanne bangare, kotun ta bayyana cewa zata sanar da ranar da zata yanke hukunci nan bada jimawa ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp