Yadda Matashi Dan Shekara 22 Ya fado Daga Benan Kamfanin Cocoa Mai Hawa 26

IMG 20250607 WA0019

Daga Aminu Bala Madobi

An yi jana’izar wani matashiya Mai shekara 22 mai suna Feranmi Akin-Akinye wanda ya fado daga bene me hawa 26 na babban ginin kamfanin Cocoa da ke Ibadan a jihar Oyo.

Akin-Akinye, wanda ya kammala karatunsa na jami’ar Afe Babalola, Ado Ekiti, jihar Ekiti yana samun horo kan harkar tsaro ta yanar gizo a wani kamfani da ke hawa na takwas na ginin a lokacin da lamarin ya faru.

Ko da yake wasu rahotanni da kafafen yada labarai suka wallafa sun ce an kai Feranmi, zuwa Asibitin Kwalejin Jami’ar, inda aka tattaro cewa matashin mai shekaru 22 ya mutu nan take bayan ya gamu da ajalinsa.

A cewar jaridar The Nation, wata majiya da ke kusa da dangin marigayin ta ce an karbe gawarsa kuma nan take aka binne shi.

Mahaifin yaron dai yana zaune ne a kasar waje, yayin da shi yaron da wasu ’yan’uwan sa biyu ke karkashin kulawar mahaifiyarsu, wacce shahararriya ce kuma ana mutunta su a unguwar.

Yadda Akin-Akinye ya fado daga benen Kamfanin Cocoa ya mutu?

Marigayin ya koma bakin aiki ne a ranar litinin da ta gabata, kuma ya tafi tare da wasu abokan aikinsa zuwa saman benen domin dora tuta a bangon ginin a wani bangare na aikin da ya shafi aiki.

Yayin da ake gudanar da aikin, an fahimci cewa wani Dan karamin firam na katako ɗin da ya sanya kafarsa ba shi da ƙarfi da zaiya ɗaukar nauyin shi, wanda hakan ya sa ya faɗo bisa kuskure daga hawa na 24 a wurin.

“Nan da nan aka garzaya da shi asibitin jihar Adeoyo amma tuni aka tabbatar da mutuwar sa saboda kan sa da wasu sassa na jikin sa sun samu lahani kafin fadowar sa kasa.

Ga Masu Son Bada Talla A Kira   +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *