Yadda Hukumar Yaki da Cin Hanci Da Rashawa Ta Kano Ta Bankado Sama Da Biliyan 50 Da Gwamnatin Ganduje Ta karkatar

Screenshot 20240415 155804 (1)

Daga Aminu Bala Madobi

Shugaban hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, ya ce hukumar ta yi nasarar gano sama da Naira biliyan 50 na kudin kananan hukumomi da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya karkatar.

Alfijir Labarai ta rawaito Magaji Rimingado, wanda ya bayyana a shirin talabijin na Arise a karshen mako, ya ce kudaden da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta samu nasarar ganowa sun kai rabin Naira biliyan 100 da aka ware wa kananan hukumomin jihar.

Muhuyi ya kara da cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gano akasarin kudaden ne a asusun wasu mutane uku.

“Mun gano makudan kudaden da aka karkatar zuwa asusu daban-daban na daidaikun mutane, daga nan muka kwashe kudaden a cikin tsabar kudi zuwa gidan gwamnatin jihar tare da wanda aka taske da injin kirga kuma aka canza su zuwa dala.

Hukumar takuma bayyana cewa ta tare mutane kusan 200 wadanda suka ce gwamnatin Ganduje ta bukaci su rubuta “motoci sun siya a asibitoci, magunguna duk karya ne kuma ba su yi ba. Ta haka ne muka tattara sama da Naira biliyan 51. Muna da kwakkwaran shaidu na kai kara kotu.”

Da yake magana kan hannun matar Ganduje, Hafsat a cikin wannan zamba, shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, ya ce matar tsohon gwamnan ce nada hannu kan kusan dukkanin asusun ajiyar da ke da alaka da cin hanci da rashawa.

Ya kuma yi zargin cewa Ganduje ya sayar da kadarorin Kano a farashi mafi gurguncewa ga iyalan su a zamanin mulkinsa.

A shekarar 2021, Abdulazeez ya kai Hafsat, mahaifiyarsa, zuwa hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) bisa zargin almundahana da ya shafi filaye

A shekarar 2018, Ganduje ya shiga cikin wani faifan bidiyo mai cike da kunya, inda ake zargin yana karbar kudade dala a cikin abin da aka ce cin hanci ne daga hannun ‘yan kwangilar ayyukan gwamnati.

An gan shi yana karbar dalolin kafin ya mirgina su cikin farar rigar sa, “babanriga,” a daya daga cikin jerin yarjejeniyoyin da ake zargin an kulla na tsawon watanni da dama.

Ana zargin Ganduje da karbar kudi har Naira miliyan 750 (kimanin kashi 25 cikin dari) a kan sama da Naira biliyan 3 da dan kwangila daya.

Baya ga takaicin binciken badakalar da majalisar dokokin jihar ta yi, Ganduje wanda a lokacin yana da kariya daga tuhuma a matsayinsa na gwamna a karon farko ya lashe zabensa a karo na biyu duk da badakalar cin hanci.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *