Yadda Ake Tufka Da Warwara A Zaɓen Gwamna A Adamawa

Alfijr ta rawaito an hana ‘yan jarida shiga cibiyar tattara sakamakon zaben jihar Adamawa da jami’an ‘yan sanda da ke ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) suka gudanar a jihar.

An bayyana cewa, an riga an ba wa ‘yan jaridun izinin gudanar da zabukan shugaban kasa da na gwamnoni, amma jami’an ‘yan sanda sun yi watsi da su a cibiyar.

Rahotanni sun ce ‘yan sandan sun yi ikirarin cewa suna da jerin sunayen ‘yan jarida da aka amince da su wanda daga baya suka kira su shiga cibiyar tattara bayanan.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ana yunkurin dauke cibiyar tattara sakamakon zabe ta INEC daga hanyar banki zuwa yankin Dougerei na jihar.

Hakan ya haifar da zanga-zanga da magoya bayan jam’iyyar PDP suka yi inda suka sha Qalwashin yin tir da duk wani yunkuri na kawo cikas ga sakamakon zaben gwamna.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, tuni wasu daga cikin jami’an tattara bayanan na cikin cibiyar tattara kuri’u yayin da ake ci gaba da tantance kuri’u.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a1

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
0Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *