
Alfijr ta rawaito Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta ce ta kama wasu mutane 12 da ake zargi da sayan kuri’u a karin zaben da aka yi ranar Asabar a jihohin Kano da Katsina.
Kwamandan EFCC na shiyyar Kano, Faruk Dogondaji, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, a wata hira da ya yi da manema labarai cewa, an kama wadanda ake zargin da tsabar kudi Naira miliyan 1.5 a jihohin Kano da Katsina.
A cewarsa, an kama mutane 10 ne a karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano, biyu kuma a karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina.
Dogondaji ya ce an kama wadanda ake zargin ne a lokacin da suke kokarin jawo masu kada kuri’a da kudade a wasu rumfunan zabe.
Ya ce an kama wadanda ake zargin su 10 ne da Naira miliyan 1,357,500 a karamar hukumar Doguwa, yayin da aka kama mutanen biyu da N242,000 a karamar hukumar Kankia.
“Har ila yau, za mu kasance a jiki a duk cibiyoyin tattarawa don hana canjin sakamako,” in ji shi.
Ya ce kasancewar jami’an da ke gudanar da zaben zai kara sahihanci ga aikin.
Kwamandan na EFCC ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu bayan bincike.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ