Yadda aka ƙaddamar da tashin sahun farko na maniyyatan Nijeriya zuwa Saudiyya

FB IMG 1746824475989

Babban mai taimaka ma shugaban kasa akan harkokin Siyasa Alh.Ibrahim Kabir Masari da shugaban hukumar AUDA-NEPAD Alh. Jabiru Tsauri sun halarci bikin kaddamar da jirgin farko na aikin Hajjin 2025 a jihar Imo.

A ranar juma’a 09-05-2025 suka isa jihar ta Imo a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa dake Owerri domin halartar bikin kaddamar da tashin alhazan zuwa kasa mai tsarki Saudiyya.

Bikin ya samu halartar manyan baki masu daraja, ciki har da Mai Girma Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma.

Sheikh Saleh Pakistan, Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa; Hajiya Olubunmi Kuku, Manaja Darakta/CEO na FAAN; Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III; Sanata Abubakar Sani Bello, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Ƙasashen Waje. da Hon.

Yayin da mahajjatan ke shirin tashi zuwa kasa mai tsarki domin wannan ibada mai girma, muna  roƙon Allah Ya kare su, Ya sauƙaƙa musu, kuma Ya karbi ibadarsu. Allah Ya albarkaci hajjin bana ayi lafiya a gama lafiya.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *