Ya Kamata Shugabannin Nijeriya Da Yawansu Su Kasance A Gidan Yari A Garkame —Obasanjo

FB IMG 1723302788686

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya ce galibin wadanda ke rike da mukaman gwamnati a Najeriya ba su da halin shugabantar kasar.

Alfijir labarai ta ruwaito Obasanjo ya kara da cewar kamata ya yi a ce sun kasance a gidan yari a halin yanzu.

Obasanjo ya yi wannan jawabi ne a gidansa da ke Abeokuta, jihar Ogun, yayin da ya karbi bakuncin ‘yan majalisar wakilai guda shida wadanda ke rajin kudirin wa’adin mulki na shekara shida, da na karba-karba na shugabancin kasa tsakanin arewa da kudu da kuma karba-karba na takarar gwamna daga cikin gundumomin sanatoci uku na kowace jihohi 36.

‘Yan majalisar dai sun samu jagorancin Ugochinyere Ikenga mai wakiltar mazabar Ideato ta Arewa da Ideato ta Kudu a jihar Imo.

Ya kara da cewar  bayan sake duba dimokuradiyyar Najeriya, akwai bukatar duba shugabanci mai nagarta.

A cewarsa, har sai shugabanni sun sauya tunaninsu kasar ba za ta taba ganin canjin da ake bukata ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *