Wani ɗan ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan da ya nemi ya miƙa masa wayar da ke hannunsa.
Alfijir labarai ta rawaito cewa a wata sanarwa da rundunar sojin Div 1 da ke Kaduna ta fitar ta ce Lt Commodre M Buba da ke kwas na shiga layin manyan sojoji ya samu fanco a tayar motarsa abin da ya tilasta masa tsayawa a daidai gadar sama ta Kawo da ke Kaduna, inda fitowarsa ke dawuya sai wani ya zo ya same shi ya nemi ya ba shi wayarsa.
Sai sojan ya nemi sanin dalilin bayar da wayar abin da ya sa mutumin ya fitar da wuƙa ya caka masa a ƙirji.
Wani ɗn sintiri ya yi ƙoƙarin ceton sojan amma shi ma mutum ya daɓa masa wuƙar a hannunsa.
An kai Lt Commodore asibitin Manalal amma kuma rai ya yi halinsa.
Sai dai kuma BBC ta tattaro cewa mutanen da ke kusa da wurin da abin ya faru sun yi wa makashin tara-tara inda suka hallaka shi shi ma.
BBC
Ga Masu Son Bada Talla A Kira +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN