Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya tsallake rijiya da baya a ranar Juma’a bayan da mayakan Boko Haram suka farmaki ayarin motarsa a Jihar Borno.
PUNCH ta ruwaito cewa Sanata mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume, ne ya bayyana haka yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin din Channels a daren Lahadi.
A cewar Ndume, tsohon Janar din da sojojin da ke tare da shi sun fada cikin kwanton bauna ne a kusa da wata barikin sojoji .
Ko da yake ba a tantance adadin asarar rayuka ba, Ndume ya bayyana cewa musayar wuta ta barke tsakanin masu harin da sojojin da ke raka Buratai.
“Muna cikin mawuyacin hali na tsaro. Kwana biyu da suka wuce, an kai wa Buratai hari a sansanin sojoji a Borno.
“Jami’ansa sun mayar da martani cikin jarumta, amma ‘yan ta’addan sun lalata wasu kayan aikin sojoji,” in ji shi.
Ga Masu Son Bada Talla A Kira +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN