Ƙungiyar Tsoffin Jami’an Ƴan Sanda a Jihar Kaduna ta bayyana shirinta na gudanar da zanga-zangar lumana ta ƙasa baki ɗaya, wadda suka lakaba wa suna “Uwa Ga Duk Wata Zanga-zangar Lumana”, a ranar 21 ga Yuli, 2025.
Shugaban ƙungiyar, Mannir M. Zaria, tare da Mataimakinsa, Danlami Maigamo, ne suka bayyana hakan bayan wani taron wata-wata da suka gudanar a Police Officers’ Mess da ke Kaduna.
Sun ce zanga-zangar na da nasaba da matsalolin fansho da suka addabi tsoffin jami’an ƴan sanda da ke cikin tsarin Contributory Pension Scheme (CPS), wanda suka ce ya jefa su cikin ƙuncin rayuwa, tozarta su ta fuskar kudi, da kuma haifar da hauhawar damuwa da mace-mace tsakanin mambobin su.
“Ba mu da zaɓi, face mu sake ficewa mu gudanar da wata zanga-zangar lumana da muka lakaba mata suna ‘Uwa Ga Duk Wata Zanga-zangar Lumana’ wadda za mu yi a ranar 21 ga Yuli, 2025,” in ji ƙungiyar.
Ƙungiyar ta tabbatar da cewa zanga-zangar za ta kasance lumana kuma za a gudanar da ita a dukkan jihohi 36 na ƙasar nan.
“A matsayinmu na ƴan ƙasa masu bin doka, za mu ci gaba da bin hanyoyin lumana wajen neman a fitar da Ƴan Sanda daga tsarin CPS har sai an saurare mu,” a cewar sanarwar.
Ƙungiyar ta nanata cewa kafa Hukumar Fansho ta Ƴan Sanda mai zaman kanta ce kadai mafita ta gaskiya don magance abinda suka kira zalunci da rashin adalci a tsarin fanshon da ake ciki yanzu.
Domin bada talla ko shawarwari a iya kiranmu a wannan lambar +2348032077835
For more information about Alfijir labarai/Alfijir news fallow here 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD