Wata Sabuwa! Ƴan bindiga Sun Sace Wani Kasurgumin Boka

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani shahararren boka ɗan asalin jihar Anambra, mai suna Chinedu Nwangwu a ɗaya daga cikin otel ɗin sa a karamar hukumar Idemili ta Arewa.

Alfijir Labarai ta rawaito Bokan da aka fi sani da Akwa Okuko Tiwaraki, na nufin ‘kwai mai karya kwaran manja’ a turance.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe mataimakansa guda biyu a lokacin da aka yi garkuwa da shi a daren Lahadi.

Wata majiya ta ce mutumin wanda ake kyautata zaton yana ɗaya daga cikin bokaye mafiya karfi a jihar ta Anambra, an yi garkuwa da shi cikin sauki a otal ɗin sa mai suna Triple P Hotel, tare da bindige wasu mukarraban sa guda biyu har lahira.

Ana kuma kallon Akwa Okuko Tiwaraki a matsayin mai maganin gargajiya mafi kuɗi a jihar.

A 2022 ya gina tare da ƙaddamar da otal guda biyu, waɗanda aka ɗauka a matsayin mafi girma a Oba.

Majiyoyi, sun ce sace shi ya janyo ce-ce-ku-ce da kuma raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa yana ɗaya daga cikin bokaye mafiya karfi.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *