Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da cafke wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne a yunkurin su kai mummunan hari gidan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a Yola, jihar Adamawa.
Alfijir Labarai ta rawaito Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, Suleiman Nguroje, ya shaida wa SaharaReporters a safiyar yau Litinin cewa, a ranar Lahadi jiya ne jami’an rundunar suka kama wasu ‘yan ta’adda biyu da ake zargin su da hannu wajen shirin tada Bam a gidan Atiku Abubakar inda nan take aka mika su ga sojoji domin ci gaba da bincike.
“Eh, an kama wani Jibrilla Mohammed a gidan tsohon mataimakin shugaban kasa da ke Yola, kuma a lokacin da muke yi masa tambayoyi mun samu nasarar cafke dan uwansa da suke da hannu a cikin wannan shiri.
“Mun mika su ga sojoji, domin su bincike su sosai kan laifin ta’addanci da muka same su dashi,” inji shi.
Atiku, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa a 2023, a halin yanzu yana kalubalantar zaben shugaban kasa Bola Tinubu a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa; bayan da ya sha kaye a zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb