Wata Jami’a Ta Kori Malamai 2 Da Ma’aikata 9 Bisa Cin Zarafin Ɗalibai

Alfijr ta rawaito hukumar gudanarwar Jami’ar Ambrose Alli, AAU da ke Ekpoma a Jihar Edo ta kori ma’aikatanta 13 na ɓangaren koyarwa da na gudanarwa bisa wasu laifuka da suka hada da ƙaryar shekaru, zamba, karɓar kudi daga hannun ɗalibai da kuma cin zarafi tare da lalata da ɗalibai.

Mukaddashin shugaban jami’ar, Farfesa Asomwan Adagbonyin, ya ce sun yanke hukuncin ne bisa shawarar kwamitin ladabtarwa na jami’ar da ta same su da aikata laifukan.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da rahoton kwamitin ga shugaban babban kwamiti, Andrew Olotu, da mambobin sa a jiya Litinin a birnin Benin.

Ya kuma kara da cewa ma’aikatan da abin ya shafa sun fito ne daga tsangayar kimiyyar likitanci, kimiyyar dakin gwaje-gwaje na likitanci, sashen jinya, sashin injiniyanci, tsangayar shari’a da kimiyyar siyasa da dai sauransu.

Hakazalika kwamitin ladabtarwa ya ba da shawarar cewa “ya kamata a kai rahoto ga jami’an tsaro game da aikata laifukan da ma’aikatan suka yi.” In ji shi.

Adagbonyin ya ce an bada shawarar korar wani malami daga aiki bayan an same shi da laifin karbar kudade, Naira dubu 32,000 da Naira dubu 52,000, ya kara da cewa an kori daya malamin da aka sameshi da laifin lalata.

Ya ce, “Malamin ya yi ikirarin cewa ya nuna buƙatar sa ga dalibar me kawai, amma ya je cocin da take ibada don bata hakuri. Daga baya a ka canja wa yarinyar wani malamin.

“Amma daga cikin shari’o’in ladabtarwa 209 da aka samu, kwamitin ya kammala 132 daga cikin kararrakin, yayin da shari’o’i 77 ke jira.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *