
Alfijr ta rawaito Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya buƙaci majalisar dattawa ta sahale masa ya maida wa gwamnatin Borno zunzurutun kuɗi biliyan N16bn.

Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, shugaban majalisar dattawa ne ya karanta wasiƙar buƙatar Buhari a zauren majalisa ranar Talata.
A wasiƙar, Buhari ya ce gwamnatin Borno karƙashin Babagana Zulum ta fara tare da kammala wasu titunan gwamnatin tarayya, don haka ya dace ya biya kuɗin ta hanyar sabon tsarin da FG ta kafa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ