Wata Ƴar Shekaru 21 Ta Shiga Komar Yan Sanda Kan Zargin Kashe Mijinta Da Wuka

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, Maimuna ta amsa laifin ta a yayin da ake gudanar da bincike.

Alfijir Labarai ta rawaito Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama Maimuna Suleiman ‘yar shekara 21 da ke unguwar kofar Dumi a cikin birnin Bauchi bisa zargin kashe mijinta da wuka.

A cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar, mukaddashin jami’in hulda da jama’a na jihar Bauchi, Aminu Ahmed, ya bayyana cewa jami’an tsaro da ke hedikwatar ‘yan sandan yankin sun kama su ne biyo bayan bayanan da suka samu a ranar 5 ga watan Yulin 2023.

Daga karshe jami’an ‘yan sandan da ke karkashin jagorancin jami’in ‘yan sanda na DSS suka garzaya zuwa wurin da lamarin ya faru a inda suka kai dauko da wanda ake zargin zuwa Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), Bauchi domin kula da lafiyarsu.

Rahotanni da aka samu daga likitocin kiwon lafiya sun tabbatar da cewa wanda aka kashe ya mutu ne sakamakon rauni da ya samu a kirjinsa, yayin da wadda ake zargin ta samu kananan raunuka a cikinta,” in ji sanarwar ‘yan sandan.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Maimuna ta amsa laifin ta a yayin gudanar da bincike.

Rundunar ‘yan sandan ta kara da cewa, “Bincike na farko da aka gudanar ya nuna cewa wadda ake zargin (Maimuna Suleiman) ta daba wa mijinta Aliyu Mohammad mai adireshin daya wuka a sakamakon wata hatsaniya da ta shiga tsakaninsu a ranar 5 ga watan Yuli, 2023 da misalin karfe 1800 a gidan aurensu.

Yayin da ake yi mata tambayoyi, wanda ake zargin ta amsa laifin.

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sanda, CP Auwal Mohammed ya umurci hukumar binciken manyan laifuka ta jihar da ta dauki nauyin lamarin domin ci gaba da gudanar da bincike tare da gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala bincike.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *