Gwamnan Ya Naɗa ‘Yar Sa A Matsayin Sabuwar Kwamishiniya

Daga Aminu Bala Madobi

Majalisar dokokin jihar Osun a ranar 7 ga watan Yuli, 2023, ta tabbatar da jerin sunayen kwamishinoni 25 da aka mika wa majalisar domin tantancewa tare da tabbatar da su ga gwamna Ademola Adeleke.

Alfijir Labarai ta rawaito Kakakin majalisar, Adewale Egbedun, wanda ya bayyana sunayen a yayin zaman majalisar ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Ya ce kwamishinoni 25 da aka nada sun hada da Oladosu Babatunde, Bayo Ogunbamgbe, Sesan Oyedele, Kolapo Alimi, Soji Adeigbe, Moshood Olagunju, George Alabi da Sunday Oroniyi.

Sauran sun hada da Abiodun Ojo da Bashir Salami da Moruf Ayofe da Sola Ogungbile da Bunmi Jenyo da Ayo Awolowo da Wole Bada da Dipo Eluwole da Rasheed Aderibigbe da Moruf Adeleke da Adeyemo Ademola da Olabiyi Odunlade da Jola Akintola da Mayowa Adejorin da Adenike Adeleke da Tola Gani Ola-Oluwa.

Adenike Adeleke tauraruwar Instagram ce wacce ke amfani da dandalin don tallata kayan kwalliya da rayuwarta ta yau da kullun.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *