Wasu Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutune Huɗu A Jihar Bauchi

Alfijr ta rawaito rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, ta tabbatar da kashe wasu mutum huɗu da ‘yan bindiga suka yi a anguwar Gambari Sabon-Layi da ke karamar hukumar Tafawa Balewa na jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Wakili, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Lahadi.

Ya bayyana cewar ‘yan bindigar sun afkawa unguwar ne da tsakar daren ranar Asabar, sannan suka yi garkuwa da mutum ɗaya.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aminu Alhassan, ya bayar da umarnin gudanar da bincike don kama waɗanda ke da laifi. In Ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *