Wani Miji Ya Nemi Matarsa Ta Bashi Miliyan 10, Kafin Ya Saketa A Kano

Alfijr ta rawaito wata amarya mai suna Fatima Bashir Khalil wadda aka fi sani da ‘Yar Albarka ta bayyana a gaban wata shari’ar shari’ar jihar Kano, da ke zamanta a unguwar Post Office domin mijinta, Alhaji Nura Gambo, ya ki ba ta kudi domin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta wanda ya sa mijin ya kamu da rashin lafiya.

‘Yan sanda sun gurfanar da Yar Albarka a gaban mai shari’a Nazifi Adam bisa tuhume-tuhume guda uku da suka hada da tauye hakkin dan Adam da cin amana da kuma yaudara.

Lauyan maigidan, Badamasi Gandu, ya shaida wa kotun cewa wadda ake kara ta bukaci wanda ya ke karewa ya bata wasu kudade domin bikin zagayowar ranar haihuwarta, wanda mijin ya ki amincewa da hakan, kuma bayan haka ta yanke shawarar raunata shi daga bisani ta nemi a raba aurenta.

Gandu ya kuma shaida wa kotun cewa idan wanda yake karewa zai sake ta sai ta biya shi N10m da ya kashe wajen auren ta.

Sai dai a lokacin da ta ki amsa laifin da ake tuhumar ta da shi, kotun ta amince da bayar da belin ta bisa hujjar cewa har yanzu ita ce matar mai kara sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 3 ga watan Maris.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *