
Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Alfijr ta rawaito al’ummar yankin Janyau da ke karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara, sun wayi gari cikin tashin hankali da jimami bisa samun labarin yunkurin kashe wani matashi mai suna Suleman Ahmad dan shekara bakwai da wani likita makwabcinsu ya yi, saboda kawai ya ga Suleman da abokinsa suna jifan bishiyar Zaitun da ke kofar gidansa.
Da yake bayyana hakikanin abin da ya faru, mahaifin yaron Malam Ahmed Tijjani ya shaida wa manema labarai cewa, makwabcinsa wanda ma’aikacin asibitin Sarki Fahad ne, Malam Lawali Musa, a ranar Larabar da ta gabata ya kama yaronsa ya shiga da shi cikin gidansa inda ya yi masa dukan tsiya, cikin rashin tausayi .
Ya ce “Lokacin da matata ta ji wannan mummunan lamari, sai ta garzaya gidan makwabcina, ta same shi ya kulle yake gidan yana dukan yaron da ba shi da laifi, sai da muka bude kofar da karfi muka ceto yaron.

Ya Kara da cewa “Mun kai maganar ofishin ‘yan sanda mafi kusa da Janyau Outpost, amma saboda fargabar haka muka kai rahoton lamarin ga masu kare hakkin bil’adama reshen Gusau, kuma suka gaggauta kai karar ofishin ‘yan sanda ta tsakiya.
Ya ce “Muna kira ga dukkan hukumomin da abin ya shafa da su taimaka wajen ganin wanda ya aikata laifin ya fuskanci doka da nufin ya zama mai hana wasu, duba da yadda dana shi ne mutum na uku da wannan mutumin ya yiwa irin wannan lahani saboda itacen zaitun da ya shuka.
“Mun gano cewa kusan ko’ina a jikin Suleman Ahmad akwai burbushin sanda da suka hada da kansa da fuskarsa da kirjinsa da bayansa, wanda hakan ya sa ya kasa gane kowa, Wanda hakan yana iya shafar bangaren kwakwalwarsa.
Da aka tuntubi ko’odinetan kare hakkin bil’adama na jihar Zamfara, Kwamared Salisu Umar, ya shaida wa manema labarai cewa, an kawo musu karar yunkurin kisan kai, kuma nan take suka kai kara ofishin ‘yan sanda na Gusau.
Ya ce “Kamar yadda nake magana da ku a yanzu, wanda ya aikata laifin yana hannun ‘yan sanda kuma ana gudanar da bincike, kuma a namu bangaren mu tabbatar an yi wa Suleman Ahmed mai shekaru bakwai adalci.
“Mun samu labarin cewa mai laifin Lawal Musa ya yi wa wasu kananan yara guda biyu irin wannan mummunar dabi’a saboda bishiyar Zaitun da ke kofar gidansa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ