Tufka Da Warwara! Gwamnatin Najeriya Ta Musanta Zancen Karin Albashin Ma’aikata

Gwamnatin tarayya ta ce rahoton cewa shugaban kasa Bola Tinubu zai sanar da karin albashin ma’aikata a ranar murnar samun ‘yancin kai ba gaskiya bane.

Alfijir Labarai ta rawaito Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba ta hannun Mista Olajide Oshundun, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar.

Lalong ya kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da rahoton, yana mai jaddada cewa, kage ne kawai da yan kafofin sada zumunta suka yi domin yada muradunsu.

An jawo hankalin Ma’aikatar Kwadago da aiki kan rahotannin da ke yawo a yanar gizo na cewa Shugaban kasa zai ba da sanarwar bayar da kyautar albashi da kuma jin dadin ma’aikata yayin jawabinsa na ranar samun ‘yancin kai na ranar 1 ga Oktoba.

Rahoton wanda aka ce ya samo asali ne daga wata hira da aka yi da Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar, ya yi ikirarin cewa an shirya wani taro na karshe a ranar Talata tsakanin Gwamnatin Tarayya da Ma’aikata don dakile yajin aikin da ake shirin yi.

“Muna so mu bayyana a fili cewa rahoton karya ne kuma yaudara ne kamar yadda babu wani lokaci da Daraktan Yada Labarai ya bayyana irin wannan magana” in ji shi.

Ya kara da cewa, don kawar da shakku, yana da muhimmanci a jaddada cewa Daraktan yada labarai a ma’aikatar ba ya magana da shugaban kasa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *