Tsuntsun Da Ya Ja Ruwa: Iran ta kai hari kan sansanonin sojin Amurka a kasashen Jordan da Bahrain

FB IMG 1781105573463

Iran ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da ke Jordan da Bahrain a ranar Laraba, tare da gargadin kasashen yankin Tekun Fasha cewa suna da alhakin hana Amurka da Isra’ila amfani da yankunansu wajen kai hare-hare kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Rahotanni sun ce hare-haren sun biyo bayan farmakin da Amurka ta kai wa Iran a matsayin martani ga harbo wani jirgin yaki mai saukar ungulu na Apache na Amurka.

Dakarun kare juyin juya halin Iran (IRGC) sun bayyana cewa sun harba makamai masu linzami masu dogon zango kan wuraren da Amurka ke amfani da su a Jordan da Bahrain.

Sai dai sojojin Jordan sun ce sun kakkabo makamai masu linzami guda biyar ba tare da an samu asarar rayuka ko barnar dukiya ba. Haka kuma Bahrain ta ce ta dakile tare da lalata wasu hare-haren sama da Iran ta kai.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *