Tsohon Shugaban Najeriya IBB Ya Bawa Matasan Kasar Nan Wasu Shawarwari

IMG 20231225 095741

Tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida ya ce babbar nasarar da ya samu a matsayinsa na Shugaban Najeriya ita ce sanin kasar da kuma yin abota a fadin kasar tare da ɗaukar tilastawa da Tattaunawa a matsayin salon shugabanci.

Alfijir labarai ta rawaito ya bayyana haka ne yayin wata Tattaunawa da ‘yan jarida a Gidansa dake Hilltop a Minna, yace zai shawarci matasa ‘yan Najeriya masu sha’awar Shugabancin kasar nan da su nemi sanin al’umma da fahimtar Najeriya da kyau.

Da aka tambaye shi da ya bayyana nasarorin da ya samu a tsawon rayuwarsa, ya ce; “Na ɗaya shine na yi wa kasa hidima sosai. Kuma nayi karatun Dan Adam iri daban-daban

“Kuna da dama a yanzu a matsayinku na Matasa, Ku san ƙasar, kuyi nazarin kasar, da al’ummar ta. Idan kun sami damar yin hakan a gaskiya zai taimaka matuka wajen saukaka muku shugabancin kasar nan,” inji shi.

“Don haka dole ne ka yi karatun Ɗan adam Domin ka fahimci shi, kuma dole ne ka kasance mai tausayi.

Wani lokaci rashin tausayi na hana gudanar da abubuwa yadda ya dace.

Amma akwai hanyoyi da yawa da zaku bunƙasa ta yadda za ku iya cimma wasu abubuwa, wasu kuma ka roƙe su, wasu ka tursasa su da Sauransu.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *